Gesamtlänge aller Episoden: 2 days 3 hours 38 minutes
Shirin ya duba yadda Bahaushe da masu mulkin mallaka suka sauya wa yankuna ya yi tasiri a bunkasar al'adun matunen yankunan da abin ya shafa a Kamaru.
Bikin taushen fage da dubban al’ummar garin Tsangaya da ke karamar hukumar Albasu a jihar Kano da ke Najeriya
Al'ummar Jamhuriyar Nijar na ci gaba da jimamin rasuwar Alhaji Mahaman Kanta fitaccen dan Jarida kuma wakilin Deutsche Welle na farko a Jamhuriyar Nijar.
Ko kun san Kabilar Sayawa a jihar Bauchi da ke Najeriya, na da irin nata tsarin yadda take gudanar da bikin aure? Shirin Taba Ka Lashe
Shirin ya duba gasar karatun alkurani da aka shirya a jihar Yobe domin zabo gwarzaye da za su wakilci Najeriya a gasar duniya da ake yi, inda aka samu manyan baki da Sarkin Musulmin Najeriya.
Shirin ya duba bikin Hausa Kirista da aka saba gudanarwa a duk ranar 26 ga watan disambar kowace shekara sakamakon kirisimeti. Za mu ji yadda bikin ya samo asali a cikin bukukuwan al'adun Hausawa da ma yadda aka gudanar da shi.
Shin kun san tarihin Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja mazan fama a shirin harkokin wasan kwaikwayo a arewacin Najeriya?
Ko kun san cewa marigayi Shehu Usman dan Fodiyo ya rubuta tarin litattafan ilimi, shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai.
Kabilar Dagomba guda ce daga cikin kabilun da ke da matukar tasiri a arewacin Ghana kuma ta yi biki nadi a birnin Kolon na Jamus.